Ruwa Yayi Gyara a Jigawa, Gidaje 50 Sun Rushe, Mutane 200 Sun Rasa Matsugunnai

0 220

Ambaliyar ruwa ta rusa sama da gidaje 50 tare da raba mutane sama da 200 da matsugunnansu a Yalleman da Dakayyawa na Karamar Hukumar Kaugama a Jihar Jigawa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Jami’in Hulda da Jama’a na Karamar Hukumar, Alhaji Fahad Muhammad, ne ya shaidawa manema labarai a Kaugama cewa, ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon wani  ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka fara misalin karfe 4 na yammacin Litinin har zuwa karfe goman dare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: