Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa ya ziyarci Gwamna Namadi

0 207

Sabon Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jigawa, CP Ahmed Tijjani Abdullahi psc, ya ziyarci Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi FCA a Gidan Gwamnatin dake Dutse, jiya litinin.

Da yake jawabi, CP Abdullahi Tijjani ya yaba da irin goyon bayan da gwamnatin jihar ke baiwa rundunar ‘yan sandan.

A nasa bangaren, Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi FCA, ya yi maraba da CP zuwa jihar tare da ba shi tabbacin bayar da hadin kai da goyon baya ga ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro baki daya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’ummar jihar Jigawa. CP Tijjani wanda ya samu rakiyar tawagarsa, ya godewa Gwamnan Mallam Umar Namadi bisa irin tarbar da ya yi masa tare da baiwa rundunar ‘yan sandan tabbacin hadin kai ta hanyar bude kofarsa domin taimakawa ‘yan sanda wajen dakile miyagun laifuka a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: