Sama da Mutum Dubu 80 Ne Ke Bukatar Tiyatar Zuciya Kowacce Shekara a Nigeria.

0 122

Ƙungiyar ƙwararrun likitocin zuciya da jijiyoyin jini ta Najeriya (ACTSON) ta ce fiye da ‘yan Najeriya dubu 80 ne ke buƙatar tiyatar zuciya a kowacce shekara.
Shugaban ƙungiyar Dakta Uvie Onakpoya, ne ya bayyana haka a Abuja a lokacin taron ƙungiyar na shekara-shekara.
Ya ce cutukan da ke da alaƙa da zuciya da jijiyoyin jini ne ke kan gaba wajen haddasa yawan mace-mace fiye da kowacce cuta a duniya.
Dakta Uvie ya ce yara takwas cikin kowanne 100 da aka haifa na ɗauke da cutukan da suka shafi zuciya.
Ya ƙara da cewa a Najeriya fiye da yara dubu 55 ake haifa da cutar zuciya a kowacce shekara.
Shugaban ƙungiyar likitocin zuciyar ya ce a shekarar da ta gabata mutane 212 ne kaɗai aka yi wa tiyatar zuciya, sakamakon tsadar tiyatar da sauran matsaloli.
Dakta Uvie ya ce ƙungiyar ta sha yin kira ga hukumomi da su yi dokar da za ta sauƙaƙa yin tiyatar zuciyar.
Ta yadda a cewarsa masu ɗauke da jinyar za su samu sauƙi wajen zuwa asibitocin gwamnati da masu zaman kansu domin yi musu tiyatar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: