Sanata Ndume ya nemi gwamnatin Najeriya da ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ‘yan Boko Haram

0 85

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu Aliu Ndume ya nemi gwamnatin Najeriya da ta bayyana sunayen masu musayar kudaden waje na ‘yan canji 400 da tace ta kama saboda zargin daukar nauyin ‘yan Boko Haram.

Ndume ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja.

A baya kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya ce gwamnati ta kama wasu ‘yan canji da ke taimakawa ‘yan Boko Haram da kudade, kamar yadda jaridar the Cable ta rawaito.

Da yake mayar da martani kan Batun, Ndume ya ce ya zama dole gwamnati ta bayyana mutanen da ta kama kuma a gabatar da shari’arsu a bainar jama’a.

“Fadar shugaban kasa a baya ta ce ‘yan Najeriya za su girgiza idan ta bayyana sunayen wadanda suke daukar nauyin Boko Haram,” in ji shi.

“kamata ya yi fadar shugaban kasa ta fallasa sunayensu kuma a gabatar da shari’arsu a bainar jama’a kowa ya gani.

“In akwai wadanda ba su da laifi ciki sai a kyalesu su tafi, amma a tabbatar an hukunta wadanda aka kama da laifi.”

Yana kafa hujja da shiri’arsa da aka yi masa ta zargin cewa yana taimakawa ‘yan Boko Haram, inda ya nanata cewa kamata ya yi a yi komai a bude, ba tare da la’akari da girman wadanda za a yi wa shari’arba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: