Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnatin Burtaniya da ta kara karfafa dangantakarta da Najeriya da Afirka ta hanyar kara zuba jari a sassa daban-daban domin ganin nahiyar Afirka ta samu ci gaba mai dorewa da wadata.
Tinubu ya yi wannan kiran ne a jiya a lokacin da ya karbi bakuncin sakataren harkokin wajen Birtaniya Rt Hon. James Cleverly, a ofishinsa.
Ya kuma yi kira ga Birtaniya da ta kara himma wajen inganta hadin gwiwar domin cigaba ga Najeriya da Afirka.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya tunatar da tarihin zurfafa alaka tsakanin kasashen nahiyar da kuma Birtaniya tsawon shekaru da dama.
Ya ce dole ne gwamnatin Burtaniya ta hada kai da Najeriya da sauran kasashen Afirka wajen samar da gagarumin cigaban tattalin arziki, da cigaban fasaha wanda hakan zai biya bukatun ‘yan kasa baki daya.Tun da farko, Cleverly, yace ya zo Najeriya ne domin inganta dangantakar huldar da tattalin arziki.