Shugaba Buhari ya yanka kek ɗin murnar ranar haihuwarsa a ƙasar Turkiyya

0 202

Kakakin majalissar wakilai Femio Gbajaniamila, da mataimakinsa Ahmad Wase, sun taya shugaba Muhammadu Buhari murna bisa cikar sa shekaru 79 a duniya.

A sakon taya murnar da kakakin da mataimakin sa suka fitar, sun taya shugaba Buhari murna, tare da cewa ya cimma abubuwa da yawa tun bayan fara wa’adin mulkin sa na farko a shekarar 2015.

Kakakin majalisar a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Lanre Lasisi ya fitar, ya ce ya kamata dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasar su taya shugaban kasa murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

 Ya kuma yabawa shugaba Buhari kan yadda ya sanya Najeriya a gaba.

 Ya ce shugaba Buhari ya samu nasarori da dama a matsayinsa na mutum da kuma a matsayinsa na shugaba mai hali da rikon amana.

 Hakazalika, mataimakin kakakin a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Umar Muhammad Puma ya fitar, ya ce shugaban ya cancanci a yi masa shari’a ta gaskiya bisa la’akari da irin nasarorin da ya samu a cikin shekaru shida da suka gabata.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da gwamnan jihar Legas Babjide Sanwo-Olu sun taya shugaba Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar tasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: