Shugaba Buhari yace Najeriya a shirye take ta haɗa hannu da ƙasar Turkiyya domin magance matsalolin tsaro

0 151

Shugaban kasa Muhammadu buhari yace nageria a shirye take ta hada hannu da kasar turkiyya domin magance matsalolin tsaron da suka addabai kasar nan.

Buhari ya bayyana hakan ne a yau jumaa yayin wata ganawa da dabbaka huldar deplomasiyya da shugaban kasar turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a babban birnin kasar Santanbul.

Buhari yace dangantaka tsakanin kashen biyu zai cigaba da karuwa a irin salon nan na ban gishiri na baka manda, ya kara da cewa yana dakon tallafin kasar turkiyya domin magance matsalar tsaro.

A cewar sanarwar wacce mai magana da yawun shugaban kasa mallam Garba Shehu ya fitar, tace buhari ya bayyana kasar turkiyya a matsayin wacce ke da kwarewa wajen magance matsalolin tsaro.

Da yake jawabi tun da farko shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan yace kasar sa a shirye take ta taimaki Najeriya wajen dakile matsalar tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: