Shugaba Tinubu ne zai bayyana matsaya dangane da batun aikin kamfanin jiragen saman Najeriya

0 148

Ministan Sufurin Jiragen sama na kasa Festus Keyamo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ne zai bayyana matsaya dangane da mataki na gaba kan batun aikin kamfanin jiragen saman Najeriya.

Keyamo ya shaidawa hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan taron majalisar zartarwa na kasa na wannan makon a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Ministan ya ce ba zai zama “rashin gaskiya ba” gwamnatin Tarayya ta kulla yarjejeniyar da zata bai wa wata kasa ikon mallakar masana’antar zirga-zirgar jiragen sama a Najeriya.

Watanni shida bayan wani gagarumin biki a ranar 26 ga Mayu, 2023, domin murnar zuwan jirgin saman kasar nan a karon farko, kirar Boeing 737-800, jirgin ya samu cikas tun a wancan lokacin. Sai dai Keyamo ya bayyana cewa wasu bayanai na yarjejeniyar da aka rattabawa hannu da manyan masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar, kamfanin jiragen saman Ethiopian Airlines, na bukatar wani nazari na tsanaki, domin amfanin al’ummar kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: