Shugabannin addinai sun nuna damuwa dangane da harin da ya kashe mutane sama da 90 a Kauyen Tudun Biri

0 140

Shugabannin addinai daga ‘Yankin arewacin kasar nan sun nuna damuwa dangane da harin ranar Lahadi da ya kashe mutane sama da 90 a Kauyen Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Yayinda suke kira domin a gudanar da bincike, shugabannin sun kuma bukaci a biya ‘Yan uwan wadanda harin ya rutsa da su diyya.

Sawaba Radio ta rawaito cewa harin ya rutsa da mata da Kananan yara a wurin Maulidi, lamarin da ya jikkata mutane sama da 60 daga cikin su.

Babban Malamin Addinin Islama Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da ya gudanar da bincike da kuma biyan diyya ga iyalan wadanda aka kashe.

Sannan ya jajantawa ‘Yan uwa da daukacin al’ummar Musulmi bisa wannan rashi, tare da yin Addu’ar Allah ya jikan wanda suka mutu. Shima shugaban Kungiyar Izalah ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan wannan harin, yana mai cewa baza su laminci sojojin kasar nan suna kashe ‘Yan Najeriya da basu ji ba ba su gani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: