Sufeto janar na ‘yansandan Najeriya ya yi tir da kisan jami’n rundunar da aka yi a jihar Ribas sakamakon rikicin siyasar da ke cigaba da ruruwa tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce IGP Kayode Egbetokun ya bai wa kwamashinan ‘yansandan jihar umarnin tsaurara tsaro don gano waɗanda suka aikata kisan.
Sanarwar ta ce an kashe Sufeto David Mgbada da kuma wani ɗan sa-kai Samuel Nwigwe a rikicin da ya auku tsakanin magoya ɓangarorin biyu bayan Gwamna Fubara ya rushe shugabannin ƙananan hukumomi tare da maye gurbinsu da na riƙo.
Sanarwar tace Sakamakon haka, babban sifetan yan sandan ya aika da dakarun rundunar na Intelligence Response Team (IRT) domin su taimaka wa ‘yansandan Ribas wajen kama makasan. A yau Laraba ne gwamnan ya rantsar da shugabannin bayan tun da farko majalisar dokokin jihar, ɓangaren da ke biyayya ga gwamnan, ya tantance mutanen kamar yadda Manema labarai suka ruwaito.