Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sallami shugabar farko ta Hukumar Kula da Sauyin Yanayi ta Kasa (NCCC), Dr. Nkiruka Madueke, tare da naɗa Mrs. Omotenioye Majekodunmi a matsayin sabuwar shugabar hukumar.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, 31 ga Yuli, 2025, ta bayyana cewa Majekodunmi ta maye gurbin Dr. Madueke wadda aka naɗa a watan Yuni na 2024.
Mrs. Majekodunmi ƙwararriyar lauya ce a fannin muhalli da kuma masaniyar harkokin sauyin yanayi, tana da ƙwarewar fiye da shekaru 17 wajen aiki da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa. Kafin nadin nata, ita ce mai ba da shawara kan kuɗi a hukumar NCCC, inda ta taka rawa wajen tsara manufofin sauyin yanayi na Najeriya.
A cewar sanarwar, Tinubu ya godewa Dr. Madueke bisa sadaukarwar da ta yi wajen gina tushe mai ƙarfi ga hukumar tun bayan kafa ta a 2022, a zamanin Shugaba Muhammadu Buhari.
Nadin Majekodunmi, a cewar fadar shugaban ƙasa, ya nuna kudurin gwamnatin Tinubu na mayar da hankali kan batun sauyin yanayi, tare da amfani da wannan dama wajen inganta tattalin arziki, kare lafiyar al’umma da tsaron kasa.
Hukumar NCCC dai ita ce cibiyar gwamnatin Najeriya da ke da alhakin tsara da aiwatar da manufofi kan sauyin yanayi, da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya domin cimma burin Najeriya na rage hayaƙi dake gurbata iska nan da 2060.