Tsarin da ya kunshi siyasa, diflomasiyya da kuma tsaro ya kamata a bi wajen tinkarar al’amura a Jamhuriyar Nijar

0 198

Shugabannin tsaro na kungiyar ECOWAS sun ce kamata ya yi a samar da cikakken tsarin da ya kunshi siyasa, diflomasiyya da kuma tsaro wajen tinkarar al’amura a Jamhuriyar Nijar.

Kwamitin hafsan hafsoshin tsaro na kasashen yammacin Afirka ECOWAS ne ya bayyana haka a karshen wani taron gaggawa da suka yi na kwanaki uku jiya a Abuja.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya kuma shugaban kwamitin Janar Christopher Musa ne ya bayyana hakan, ya kuma yabawa kungiyar ECOWAS bisa kokarin da takeyi wajen tabbatar da dimokuradiyya, yana mai cewa sojojin kasashen kungiyar ECOWAS suna da kwarin gwaiwar dawo da farar hula Mulki a Nijar.

Ya ce, kwamitin tare da hadin guiwar ya amince cewa akwai Babbar matsala a Nijar, da kuma bukatar gaggauta daukar matakan da suka dace.

Musa ya ce hafsoshin sojin kasar sun amince da cewa babu wasu ka’idojin dimokradiyya da bin doka da oda a yankin.

Ya yi nuni da cewa juyin mulkin da aka yi a Nijar ya nuna rashin mutunta ka’idojin da ke tabbatar da hadewar yankin da zaman lafiya. Kasashen da suka halarci taron sun hada da Togo, Saliyo, Senegal, Nigeria, Liberia, Guinea Bissau, Ghana, Gambia, Cote D’ivoire, Cape Verde da Benin yayin da Nijar, Mali, Guinea da Burkina Faso.

Leave a Reply

%d bloggers like this: