Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ya yi duk abin da zai iya kan matsalolin da Najeriya ke fama da su

0 80

Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ya yi duk abin da zai iya kan matsalolin da Najeriya ke fama da su, ba kuma zai yi sama da hakan ba.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a Abuja kan matsalolin tsaro a jiya Litinin.

Taron ya samu halartar manyan shugabannin addinai da na siyasa da na kabilun Najeriya daga sassan kasar daban-daban.

Da  yake mayar da martani Ministan yaɗa labarai Alhaji Lai Mohammed ya ce ba don zuwan Shugaba Buhari ba da matsalar tsaron Najeriya ta fi muni.

A wani taron manema labarai a Abuja, Lai Mohammed ya ce Buhari ya mayar da batun tsaro a matsayin babban ginshikin gwamnatinsa.

Ya ce magance matsalar tsaro na ɗaya daga cikin abu uku da gwamnatin APC ta fi ba fifitawa.

Ministan dai na mayar da martani ne ga masu ganin sha’anin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa a zamanin gwamnatin APC ta Buhari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: