Wasu daga al’ummar Malammadori da Kirikasamma sun nemi ɗaukin gwamnatin jihar Jigawa kan yin noma a dazukan da gwamnatin ta hana

0 299

Wasu wakilan al’ummomin garuruwa 13 na yankin Ciromari daga ƙananan hukumomin Malammadori da Kirijasamma sun nemi ɗaukin gwamnatin jahar Jigawa kan yin watsi da umarnin da gwamnati ta bayar na hana noma a dazukan gwamnati da aka bayar ba bisa ƙa’ida ba ciki harda na yankin nasu.

Buƙatar hakan nazuwane bayanda wakilan al’ummomin suka kai ziyarar taya murna tare da miƙa ƙorafe ƙorafen nasu ga Hukumar kula da manoma da makiya, Ma’aikatar kula da ƙananan hukumomi da kuma Ofishin sakataren gwamnatin jahar Jigawa kan babbar makiyayar dabbobi dake yankinna Ciromari.

Jagoran tawagar Mal. Ahmad Babangida wadda yayyi magana a madadin jama’ar yayin ziyarar tasu, yace duba da yadda gwamnan jaha ya bada umarnin dakatarda noma a makiyayu da burtalai ba bisa ƙa’ida ba, yana dakyau gwamnati tashigo cikin lamarin makiyayar Ciromari da gaggawa domin kaucewa afkuwar rikici a yankin saboda wasu manoma sunƙi bin umarnin da gwamnati ta bayar wadda hakan ke barazana ga zaman lafiyar yankin nasu.

Baya ga haka, tawagar ta sake gabatar da buƙatar dakatarda aikin tonon ƙasa da akeyi a makiyayar dubada hasarar rayuku gurin ke janyowa bugu da ƙari ga kuma canza taswirar iyakar ƙananan hukumomin Malammadori da Kirikasamma.

Tawagar ta kuma yabawa shagaban ƙarmar hukumar Kirikasamma bisa ƙoƙarin da yakeyi wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin ta hanyar ƙoƙarin dakatar da manomanda suke bijirewa Umarnin da gwamnati ta bayar.

A jawabansu daban, sakataren gwamnatin jahar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim Mamsa, kwamishinan ƙananan hukumomi na jahar Jigawa Alhaji Ahmad Garba MK da shugaban hukunar kulada manoma da makiyaya ta jahar Jigawa Dr. Salisu Abdullahi Babura sun bada tabbacin gwamnati zata shigowa cikin lamarin yankin nasu domin ɗaukar matakin daya dace suna masu cewa wannan gwamnatice da bata wasa da lamarin zaman lafiyar al’ummar ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: