Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane tara tare da kona gidaje shida a jihar Filato

0 241

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane tara tare da kona gidaje shida a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Jerry Datim, daya daga cikin shugabannin al’umma ne ya bayyana hakan ta wayar tarho ga Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa jiya a Jos.
Mista Datim, wanda shi ne shugaban kungiyar Global Society for Middle Belt Heritage, ya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar.
Mista Datim, ya yabawa jami’an ‘Operation Rainbow’ da wani jami’in tsaro a jihar, bisa daukar matatan gaggawa kan harin.
Da aka tambaye shi ko mazauna yankin sun bar garin, Mista Datim ya ce sun yanke shawarar zama tare da kare garuruwan su.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aiki na musamman na sojoji Kyaftin James Oya ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: