Wike ya nuna damuwar sa kan yadda ake tafiyar da aikin wasu hanyoyi a birnin tarayya Abuja

0 137

Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya nuna damuwar sa dangane da yadda wasu ‘Yan kwangila ke tafiyar da aikin wasu hanyoyi a fadin Birnin na Abuja.

Wike, yayin ganawar sa da ‘Yan kwangilar bayan ya kammala duba wasu ayyuka, yace ya kai ziyarar bazata ne inda ake aikin domin ganewa idon sa yadda aikin ke tafiya. Ministan, wanda ya bayyana rashin jin dadin sa dangane da aikin da aka bayar a watan Disembar shekarar 2023,tare da yin ‘yan kwangilar su gaggauta cimma yarjejeniyar da aka kulla da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: