Yan bindiga sun kai farmaki yankin Heipang dake karamar hukumar Barkin Ladi

0 258

An kashe mutane 21 yayin bindiga sun kai farmaki yankin Heipang dake karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Lamarin ya faru da dadare a lokacinda mafiya al’ummar yankin ke bacci.

Wannan harin ya faru kwanaki uku bayan an kashe wani dan kasuwa dake saida shanu a garin.

Kungiyar yan Kabilar Berom sun yi Allah wadai da wanna harin, tare da bayyana harin da cewa makiya zaman lafiya ne suka kai shi.

Mai magana da yawun dakarun sa kai na SAFE HAVEN Kaftin Ola James ya tabbatar da mutuwar mutane 17,ya kuma kyautata zaton harin da na ramuwar gayya ne. Shi ma maigana da yawun kungiyar kabilan BEROM Rwang Tengwong cikin wata sanarwa da ya fitar,yace mutane 17 aka kashe a yankin, sannan kuma yan Bijilanta sun gano gawarwakin mutane 4

Leave a Reply

%d bloggers like this: