‘Yan bindiga sun kai wa ‘yansanda hari a Jihar Katsina

0 126

‘Yan bindiga sun kai wa ‘yansanda hari a yankin ‘Yar Tsamiyar Jino da ke karamar hukumar Kankara a Jihar Katsina, inda suka kashe jami’an ‘yansanda hudu.

Daga bisani, maharan sun kone motar sintirin ‘yansandan.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, da farko, ‘yan bindigar sun shirya kai wa matafiyan2 da ke hanyarsu ta zuwa kasuwar Kankara daga yankin Mai Dabino hari.

Sai dai, mutanen yankin sun guje wa hanyar bayan samun labarin harin da ‘yan bindigar ke kokarin kai wa.

Bayan shirin farko ya ci tura, ‘yan bindigar sun karkatar da hankalinsu zuwa kauyen ‘Yar Tsamiyar Jino, inda wannan mummunan al’amari ya faru. Wannan lamari ya kara tayar da hankalin jama’a game da matsalar tsaro a yankin, amma babu wata sanarwa daga rundunar ‘yansandan Jihar Katsina.

Leave a Reply

%d bloggers like this: