‘Yan Najeriya na fuskantar barazanar tsaro

0 230

Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar, yayi kira da a hadin gwiwa tsakanin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya domin inganta tsaro da magance matsalar sauyin yanayi a kasar nan.

Muhammad Badaru ya fadi haka ne a cibiyar tsare-tsare ta kasa da ke Jos babban birnin jihar Filato, inda ya bayyana cewa yan Najeriya na fuskantar barazanar tsaro musamman sakamakon sauyin yanayi.

Ministan ya Ambato wasu tsare-tsare da zasu kara inganta karfin tsaron kasar nan da magance matsalar sauyin yanayi da ake fuskanta,inda yace ma’aikatar makamashi ya kamata da samar da tsare-tsare domin da suka shafi muhalli, yayinda majalisun tarayya su dauki nauyin magance matsalar sauyin yanayin. Anasa jawabin,daraktan cibiyar tsare-tsare ta kasa Farfesa Ayo Omotayo,ya bayyana cewa manufar taron shine samar da hanyoyin inganta tsaro da magance matsalolin sauyin yanayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: