Yayin da ake shirin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekaru biyu a ofis, hukumar CDCU da ke duba nasarorin ministoci tana kan duba sabbin bayanai domin miƙa masa sabon rahoton ayyukan ma’aikatunsa.
Bayan duba ayyukan watanni ukun farko na shekarar 2025, rahoton zai nuna irin nasarorin da kowace ma’aikata ta cim ma dangane da alkawurran da suka sa wa hannu a taron fadar shugaban kasa na bara.
Shugabar CDCU, Hadiza Bala-Usman, da tawagarta na duba sahihancin ayyuka da bayanai da ma’aikatun suke lodawa a dandalin hukumar, inda aka fara ba su maki. Wannan rahoton dai zai taimaka wajen nazarin cancantar ministocin, wanda ke nuna cewa wasu da dama sun gaza, sai dai ana sa ran shugaban kasa ba zai dauki matakin gaggawa ba sai bayan cikakken nazari.