Za’a fara tantance wadanda suka nemi aikin dan sanda na Kwansitabul a jihar Jigawa

0 218

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Jigawa tace zata fara tantance wadanda suka nemi aikin dan sanda na Kwansitabul daga ranar Litinin 8 ga wannan wata zuwa 29 ga wannan wata na Jeneru shekarar 2024.

Mai magana da yawun ‘Yan sandan Jihar DSP Lawan Shisu Adam shine ya sanar da haka a Dutse.

Yace dukkan wadanda suka nemi aikin dan sanda ta yanar gizo kuma suka samu takardar gayyata ta adireshin su na Email, zasu je ofishin hukumar domin a tantance su da kuma takardun su.

Ya kara da cewa masu neman aikin da ake aike musu takardar gayyata zasu je Shelkwatar hukumar dake Dutse sanya da Farar riga da rigi mai karamin hannu da kuma takardun su.

Ya bayyana cewa duk mai neman aikin na dan sandan da bai je da abubuwan daka nema ba, ba’a tantance shi ba.

A cewar sa, aikin tantancewar  ba’a karbar ko sisi.

Kazalika,ya gargadi masu neman aikin dangane da jinkirta zuwa ko makara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: