MAJALISSAR ZARTARWAR JIHAR JIGAWA TA AMINCE DA KASHE KUDI SAMA DA NAIRA MILYAR 500 WAJEN FADADA NOMAN RANI

0 578

Majalissar zartarwar jihar Jigawa ta amince da kashe kudi sama da Naira Milyan 500 domin fadada noman rani a warwade dake yankin karamar hukumar Dutse.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa da wasanni Hon. Sagir Musa ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalissar karkashin Gwamna Umar Namadi a gidan Gwamnati dake dutse.

Haka kuma kwamishinan ya kara da cewa majalissar ta sake amincewa da kudirin sake saka hannun jarin jihar a kammfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO.

Sagir Musa ya kuma ce majalissar ta sake tattaunawa tare da amincewa da kashe sama da Naira Milyan 569 don samar da kayan makaranta wato uniform ga yara mata dubu ashirin (20) a jihar tare da samar da kujeru a kalla dubu 3,900 a makarantu daban-daban na jihar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.