Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce har yanzu ba ta karɓi kwafin hukuncin kotun tarayya da ya soke shugabancin jam’iyyar ADC karkashin David Mark, tare da rushe zaɓen fidda gwani da ya samar da ’yan takararta ba.
Hukumar ta bayyana cewa ba za ta ɗauki mataki kan hukuncin ba har sai ta karɓi kwafinsa na hukuma.
Kwamishinan INEC na ƙasa, kuma shugaban kwamitin yaɗa bayanai da wayar da kan masu zaɓe, Malam Mohammed Kudu Haruna, ya ce hukumar ba ta tattauna batun ba, domin ba a miƙa mata hukuncin kotun ba.
Ya ce ana iya ɗaukar kusan mako guda kafin a samu sahihin kwafin hukuncin kotu.
Wannan na zuwa ne bayan yaɗuwar rahotannin cewa INEC ta cire sunayen tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Rotimi Amaechi, daga shafinta na intanet.
Sai dai binciken da jaridar Daily Trust ta ce ta gudanar a shafin hukumar ranar Juma’a ya nuna cewa har yanzu sunayensu na nan.
A ranar da ta gabata ne Mai shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya soke shugabancin ADC karkashin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tare da rushe matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen fidda gwani da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na 2027.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban ADC na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar yana ƙalubalantar shugabancin Mark.
Kotun ta ce tsarin da aka bi wajen kafa shugabancin bai cika ƙa’idojin zaɓen cikin gida na dimokuraɗiyya da dokar zaɓe ta tanada ba.
ADC ta yi watsi da hukuncin, tana mai cewa za ta ɗaukaka ƙara, yayin da Atiku ma ya ce zai kalubalanci hukuncin a kotu, kuma kamfen ɗinsa na shugaban ƙasa zai ci gaba.