Peter Obi ya bata takararsa da karerayi – Shattima

0 15

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya zargi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da amfani da ƙarya da alkaluman da ba su da tushe a siyasarsa, yana mai cewa hakan ya jawo masa koma baya a takarar 2027.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin zaɓen jam’iyyar APC a birnin Uyo, jihar Akwa Ibom, ranar Juma’a.

Ya ce kalaman Obi ba sa ƙara jan hankalin ’yan Najeriya kamar yadda yake a baya, yana mai zargin cewa ya yi asarar amincewar da yake da ita a wurin jama’a.

Tun da farko, Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya gudanar.

Ayyukan sun haɗa da sabon ginin tashar jiragen sama ta Victor Attah da ke Uyo.

Tinubu ya bayyana ziyarar tasa a matsayin komawa gida, inda ya tuna irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa garin Eket a lokacin da yake aiki da kamfanin Mobile.

Shugaban ya kuma yaba wa Gwamna Umo Eno, yana mai cewa jajircewarsa wajen ci gaban jihar ce ta sa gwamnatin tarayya ta amince da filin jirgin saman Victor Attah ya riƙa karɓar jiragen ƙasashen waje.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner