A Guri da ke jihar Jigawa an kashe naira dubu 600 wajen samar da kayan aiki ga ma’aikatan tsaro da masinjoji

0 124

A ƙaramar hukumar Guri da ke jihar Jigawa, an kashe naira dubu 600 wajen samar da kayan aiki ga ma’aikatan tsaro da masinjoji guda 25 domin inganta ayyukan yau da kullum.

Shugaban ƙaramar hukumar, Abubakar Umar Danbarde ne ya bayyana hakan yayin raba kayan a dakin taro na sakatariyar hukumar, inda ya ce gwamnati za ta ci gaba da samar da kayan aiki ga dukkan ma’aikata don sauƙaƙa musu ayyukansu.

Ya bukaci ma’aikatan da su riƙa halartar wurin aiki da wuri da kuma tafiya daidai lokacin tashi aiki, yana mai jaddada cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba kan duk wanda ya ki cika aikinsa yadda ya kamata.

A nasa jawabin, jami’in kula da ma’aikata Bala Isma’il, ya bayyana cewa masu tsaro sun samu unifom, da baka da kibau, da adda da fitilu, yayin da masinjoji suka samu farar riga da jar hula domin bambance su cikin sauƙi.

Leave a Reply