Abin da ya sa Adeleke ya doke APC a zaben Gwamnan Osun
Ga jam’iyyar APC, zaɓen Gwamnan Jihar Osun na 2026 ya kamata ya kasance wani sabon fafatawa da aka shirya sosai. Bayan shekaru huɗu da ta rasa jihar ga Gwamna Ademola Adeleke, jam’iyyar ta dawo da sabon ɗan takara, Bola Oyebamiji.
Gwamnatin Tarayya ta mara wa takararsa baya, yayin da yaƙin neman zaɓensa ya dogara sosai kan tasirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda wasu ke cewa dan asalin Osun ne, da kuma tsarin siyasar APC na ƙasa.
Sai dai bayan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kammala tattara sakamakon zaɓen ranar Lahadi, Adeleke na Jam’iyyar Accord, ba kujerarsa kawai ya kare ba, ya ba wa dan takarar APC tazarar tazarar ƙuri’a 66,252.
Adeleke, ya ya samu ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815. Adeleke ya lashe ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji ya samu nasara a 11.
Wannan sakamakon ya haifar da tambaya kan yadda ɗan takarar APC ya gudanar da yaƙin neman zaɓensa: Me ya sa jam’iyyar mai mulki ta kasa amfani da manyan fa’idodin siyasar da take da su wajen samun nasara?
Amsar na iya kasancewa haɗuwar wasu dalilai da suka haɗa da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar, tasirin gwamnatin tarayya, damar da kasancewar Adeleke a kan mulki ta ba shi, dabarun yaƙin neman zaɓensa da kuma irin salon siyasar masu zaɓe a Osun.
EFCC ta yi wa APC illa
Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi tasiri a siyasa a ƙarshen yaƙin neman zaɓen shi ne matakin Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) na daskarar da asusun Gwamnatin Jihar Osun.
Hukumar ta ce matakin na da alaƙa da binciken zargin wasu matsalolin kuɗi, inda ta musanta cewa matakin na da wata manufa ta siyasa.
Ta fuskar aikinta, EFCC na da haƙƙin binciken zargin aikata ba daidai ba kan kuɗaɗen gwamnati. Sai dai zaɓe ba ya gudana bisa bayanin hukumomi kawai; yadda jama’a ke kallon lamarin ma na taka muhimmiyar rawa.
A fagen siyasa, matakin ya yi wa APC illa. Lokacin da aka ɗauki matakin ya bai wa Adeleke wani muhimmin alfanu a yaƙin neman zaɓe, inda ya riƙa nuna cewa gwamnatin tarayya ta APC na ƙoƙarin matsa wa gwamnatinsa lamba.
Umarnin da Shugaba Tinubu ya bai wa EFCC na buɗe asusun gwamnatin jihar bai yi yawa wajen sauya wannan fahimta ba.
Rauni bayan zaɓen ɗan takarar APC
APC ta kuma shiga zaɓen da nauyin rikicin da ya biyo bayan tsarin zaɓen ɗan takararta.
A watan Disamba 2025, jam’iyyar ta hana wasu masu neman takarar gwamna shiga gasar. Hakan ya sa wani ɓangare mai yawa na lokacin yaƙin neman zaɓen jami’iyyar ya tafi wajen shawo kan rashin gamsuwa da tsarin da aka bi wajen fitar da Oyebamiji.
Tambayar ita ce ko sulhun da aka yi daga baya ya isa a dawo da cikakkiyar haɗin kan magoya bayan jam’iyyar da ake buƙata domin kayar da gwamna mai ci.
Sakamakon zaɓen dai ya nuna cewa, duk da cewa an ga sulhun a matakin shugabannin jam’iyyar, bai haifar da isasshen haɗin kai a faɗin jihar ba.
Ikon Gwamnatin Tarayya ta koma matsala
APC ta kuma fuskanci wani abin mamaki daga ɗaya daga cikin manyan ƙarfin da take da su — ikon gwamnatin tarayya.
Tsarin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar na ƙasa ya kawo manyan ’yan siyasa Osun, abin da ya nuna muhimmancin da aka bai wa zaɓen. Takarar Oyebamiji ta samu goyon bayan ƙarfin siyasar gwamnatin Tinubu.
A al’ada, irin wannan goyon baya ya kamata ya ƙarfafa ɗan takara. Amma a Osun, ya samar da wata sabuwar magana ta siyasa.
Adeleke ya shafe lokaci yana bayyana zaɓen a matsayin fafatawar da jihar ke buƙatar kare kanta daga matsin lamba daga wajen jihar.
Yayin da zaɓen ya ƙara alaƙantuwa da Abuja da manyan jiga-jigan APC na ƙasa, hakan ya sauƙaƙa wa Adeleke bayyana shi a matsayin fafatawa tsakaninsa da gwamnatin tarayya.
Wannan magana ta ƙara ƙarfi ne musamman saboda rikicin EFCC.
Adeleke kuma ya shiga zaɓen da wani abu da Oyebamiji ba zai iya samarwa da kansa ba — shekaru huɗu na gogewa a kan mulki.
Yana da ayyukan raya ƙasa da zai ƙaddamar, manufofin da zai kare da kuma alaƙar da ya gina da al’ummomi da sarakunan gargajiya.
A watannin da suka gabaci zaɓen, gwamnan ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan more rayuwa tare da aza harsashin wasu.
Tsarin siyasar Adeleke
Baya ga ayyukan gwamnati, Adeleke ya amfana da tsarin siyasar da ya daɗe yana wanzuwa kafin zuwansa kan mulki.
Iyalinsa sun kasance masu tasiri a siyasar Osun tsawon shekaru, yayin da shi kansa ya taɓa neman kujerar gwamna a 2018 kafin ya yi nasara a 2022.
Saboda haka, zaɓen 2026 shi ne karo na uku da ya shiga takarar gwamna a faɗin jihar.
Wannan ya sa ya san taswirar siyasar jihar, ya fahimci ƙarfi da raunin abokan hamayyarsa, sannan ya shafe shekaru yana gina alaƙa da ’yan siyasa da masu zaɓe.
Adeleke bai tsaya kan nasara a yankin Ede, inda yake da ƙarfi ba. Ya lashe ƙananan hukumomi 19, ciki har da manyan cibiyoyi kamar Osogbo, Ede ta Arewa, Ede ta Kudu, Iwo, Ife ta Gabas da Ife ta Tsakiya.
A Ede ta Arewa, inda yake siyasa a tushe, Adeleke ya samu ƙuri’a 35,427, yayin da Oyebamiji ya samu 10,283.
A Osogbo ma Adeleke ya samu ƙuri’a 36,480, sabanin 30,474 da Oyebamiji ya samu.
Davido ya ƙara wa Adeleke farin jini
Shigar fitaccen mawaƙin Afrobeats, Davido, cikin yaƙin neman zaɓen ta kasance wata babbar fa’ida ga Adeleke.
Shahararren mawaƙin ya ba yaƙin neman zaɓen Adeleke damar samun ƙarin farin jini, musamman a tsakanin matasa.
Ya ƙara masa farin jini a kafafen sada zumunta, ya kuma jawo hankalin matasa da na duniya kan zaɓen, ciki har da kiran gwamnatin Amurka da ta mai da hankali kan abin da ke faruwa a zaɓen.
Shi ma Adeleke ya mayar da salon rawa da mu’amalarsa ta yau da kullum da jama’a zuwa wani ɓangare na salon siyasarsa.
Abin da wasu abokan hamayyarsa ke kallon sa a matsayin alamar rashin ɗaukar al’amuran gwamnati da muhimmanci, magoya bayansa sun mayar da shi wani ɓangare na abin da suke so a tare da shi.
Maimakon ya guje wa wannan suna, yaƙin neman zaɓen Adeleke ya rungume shi.
Matsin tattalin arziki
Yanayin tattalin arziki na ƙasa ma ya kasance wata matsala ga APC. Jam’iyyar na neman jama’a su zaɓi ɗan takararta ne a lokacin da ita ce ke mulkin gwamnatin tarayya.
Yaƙin neman zaɓen Adeleke ya yi ta kwatanta gwamnatinsa da gwamnatin APC ta baya, musamman kan walwalar ma’aikata, ayyukan raya ƙasa da kuma harkokin kuɗin jihar.
Tarihin Oyebamiji ya sa wannan batu ya fi tasiri, domin ya taɓa zama Kwamishinan Kuɗi a lokacin gwamnatin Oyetola.
Saboda haka, yaƙin neman zaɓen Adeleke ya yi ƙoƙarin mayar da zaɓen ba wai kuri’ar amincewa ko rashin amincewa da gwamnatinsa kawai ba, har ma da hukunci kan yadda APC ta gudanar da mulkin jihar a baya.
Ga ’yan Najeriya da ke fuskantar tsadar abinci, raguwar ƙarfin sayayya da sauran matsalolin tattalin arziki, jam’iyyar da ke mulkin gwamnatin tarayya na iya zama wadda jama’a za su ɗora wa alhakin matsalolin da suke fuskanta.
Wannan ya haifar da yanayi mai wahala ga ɗan takarar jam’iyya mai mulki. Don haka Oyebamiji ya fuskanci aikin tallata kansa a matsayin zabin da ya dace a matakin jihar, yayin da yake ɗauke da nauyin siyasar gwamnatin tarayya da ake yawan sukar yanayin tattalin arzikinta.
Tasirin Najeem Salaam na ADC
Ɗan takarar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’a 17,180.
Ko da yake wannan adadi bai kusa kaiwa ga kalubalantar manyan ’yan takarar biyu ba, kasancewar ADC a zaɓen ya taka rawa.
Tun farko ana kallon zaɓen a matsayin fafatawa tsakanin Adeleke, Oyebamiji da Salaam.
ADC dai ba ta samu nasarar lashe ko ƙaramar hukuma ɗaya ba, amma kasancewarta ta ba masu zaɓe wata hanya ta daban a wajen manyan jam’iyyu biyu.
Ko da yake ba a da isasshen dalilin cewa ADC ce ta haddasa kayar da APC, a zaɓen da aka yanke da tazarar ƙuri’a 66,252, kasancewarta jam’iyya ta uku na daga cikin abubuwan da suka taka rawa a lissafin zaɓen.
Kasancewar Adeleke gwamna
Adeleke ya kuma samu wata fa’ida da APC ba za ta iya ƙirƙira wa Oyebamiji ba — shekaru huɗu na mulki.
Gwamnatinsa ta yi amfani da lokacin da ya rage kafin zaɓe wajen nuna ayyukan raya ƙasa da sauran ayyukan gwamnati da ta aiwatar a faɗin jihar.
Ƙaddamar da ayyukan ta ba gwamnan damar ƙara bayyana a idon jama’a. Kowace ƙaddamar da aiki ta ba shi damar mu’amala da al’ummomi, sarakunan gargajiya da ’yan siyasar yankunan, tare da nuna ayyukan da gwamnatinsa ke cewa ta aiwatar.
Muhawarar ’yan takara
Muhawarar ’yan takarar gwamna ita ma ta kasance wani muhimmiya a zaɓen.
A baya, ana sukar Adeleke kan yadda yake magana a bainar jama’a da kuma rashin nuna ƙwarewa irin ta wasu ’yan siyasar da aka saba gani.
Sai dai yadda ya yi a muhawarar ya fi yadda ake zato, hakan na iya taimakawa wajen rage ƙarfin wannan suka.
Maimakon a mayar da hankali kan rawarsa, fitowarsa a bainar jama’a da salon mu’amalarsa na yau da kullum, muhawarar ta ba shi damar nuna fahimtarsa kan harkokin mulki da kuma gabatar da kansa a matsayin gwamna mai kare ayyukan gwamnatinsa.
Masu zaɓe ne suka yanke hukunci
A ƙarshe, masu zaɓe ne suka yanke hukunci.
Zaɓen ya nuna cewa masu zaɓe a Osun a shirye suke su yi nasu lissafin siyasa, duk da kasancewar manyan ’yan siyasa, tsarin jam’iyyu na ƙasa da kuma tasirin gwamnatin tarayya.
Rahotannin cewa wasu masu zaɓe sun yi turjiya ga yunƙurin kawo cikas ga zaɓen sun ƙara nuna irin ƙudurin da suke da shi na kare mutuncin tsarin zaɓen.
A wasu rumfunan zaɓe, an ce fusatattun matasa sun kori wasu da ake zargin masu sayen ƙuri’u ne, tare da kwace jakunkunan da ke ɗauke da ɗumbin kuɗaɗe.
Wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, ya nuna wani matashi yana ɗaga wata leda da aka ce waɗanda ake zargin masu sayen ƙuri’un ne suka bari a wurin.
Daga From Taiwo George, Hameed Oyegbade (Osogbo), Peter Moses (Lagos), Promise Adagba (Akure) & Baba Martins, Sagir Kano Saleh (Abuja)