An Kama Barauniyar Jariri A Kebbi

0 44

An kama barauniyar jariri a Kebbi

Dubun wata matar aure mai shekaru 19 ta cika bayan da ta yi yunkurin sace wani jariri sabon haihuwa a Jihar Kebbi.

Asirin matar, wadda aka bayyana da Khadija Ibrahim, ya tonu ne bayan ta yi yunkurin sace jaririn a wani asibiti da ke garin Zuru a Jihar Kebbi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya ce Khadija, ta yaudari mahaifiyar jaririn, mai sabon jego, cewa ta ba ta ruwan zafi da sunan za ta yi wa jaririn haihuwa, amma sai ta tsere da jaririn.

Ya ce an gano cewa wadda ake zargrin ta dade da aure amma ba ta samu haihuwa ba, lamarin da ya sa ta cikin damuwa, ganin cewa sauran takwarorinta sun haihu.

“A sakamakon haka ta yi ta yaudarar mijinta na tsawon wata tara cewa tana da juna biyu. Bayan haihuwar jaririn Fatima Muhammad, sai Khadija ta je ta dauke jaririn ta nuna wa mijinta a matsayin abin da ta haifa,” a cewar sanarwar da rundunar ta fitar.

Daga baya jami’an tsaro suka gano inda take tare da jaririn, kuma aka kama ta. Jaririn an mayar da shi ga mahaifiyarsa.

“Ana ci gaba da tsare wadda ake zargin kuma za a gurfanar da ita a kotu da zarar an kammala bincike kamar yadda doka ta tanadar.” in ji sanarwar.

Leave a Reply