ACRESAL da ma’aikatar kare mahalli ta jihar Jigawa zasu da sa bishiyoyi 5,500,000 a fadin jihar

0 147

Shirin ACRESAL da hadin gwiwar ma’aikatar kare mahalli ta jihar Jigawa zasu da sa bishiyoyi miliyan biyar da dubu dari biyar a fadin jihar jigawa, a wnai yunkuri na magance matsalolin kwararar Hamada da sauyin yanayi.Shugaban shirin ACRESAL na jihar Jigawa Mallam Yahaya Muhammad Kafin Gana ya sanar da hakan ga manema labarai a dutse babban Birnin jiha.Mallam Yahaya Muhammad Kafin Gana yana mai cewar tuni suka yi taruka da yan kungiyoyi da kuma shugabannin sassan aikin gona na kananan hukumomi domin fitar da jaddawalin yadda zasu gudanar da dashen a kananan hukumomi.Ya ce hakan na daga cikin kudirin shirin na kawar da jihar Jigawa daga barazanar kwararowar Hamada.Shugaban shirin na ACRESAL ya kara da cewar za a dasa bishiyoyin ne a bakin titi da makarantu da asibitoci da kuma wuraren shakatawa na alumma.Yace shirin yana da cibiyoyin renon bishiyoyi 24 a fadin jihar Jigawa da ake bada dashen kyauta.A cewarsa bishiyoyin da za a dasa sun hadar da Maina da Turare da Badala da Dankanju da Goba da Kadanya da Zogale da Madachi da Kuka da kuma Tsamiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: