NiMET tayi harsashen samun ruwan sama kamar da bakin kwarya da tsawa daga yau litinin zuwa ranar laraba a fadin kasa

0 100

Hakumar lura da yanayi ta kasa NiMET tayi harsashen samun ruwan sama kamar da bakin kwarya da tsawa daga yau litinin zuwa ranar laraba a fadin kasa. Hakumar ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar jiya a Abuja, za’a samu tsawa da ruwan saman a safiyar yau litinin a sassan jihohin Kebbi, Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara, Taraba and Kaduna states. Haka kuma za’a samu makamancin yanayin da yammacin yau a sassan jihohin Taraba, Kaduna, Gombe, Borno, Yobe, and Jigawa states. A cewar hakumar za’a fuskanci matsakaicin yanayin a gabadayan a kudancin kasar nan da yammacin yau.Kazalika hakumar tace gajimarai zai lullube sararirin samaniya a gobe Talata yayin da za’a tsammaci ruwa kamar da bakin kwarya da safiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: