Akalla mutane 1,205,888 ne suka yi rijistar jarrabawar kammala sakandare ta 2023 – NECO

0 268

Hukumar shirya jarabawar ta kasa NECO, ta ce akalla mutane 1,205,888 ne suka yi rijistar jarrabawar kammala sakandare ta 2023, SSCE.

Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a Azeez Sani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.

Sani ya ce, magatakardar hukumar ta NECO, Farfesa Dantani Wushishi ne ya bayyana hakan a garin Jos, yayin da yake sa ido kan yadda ake gudanar da jarabawar a wasu makarantun, inda ya ce a cikin wannan adadi, dalibai 601,074 maza ne yayin da 584,814 mata ne.

Magatakardar ya ce jarrabwar shekarar 2023 ta SSCE da za a kammala mako mai zuwa ita ce mafi kyawun tsari a cikin ‘yan shekarun nan da suka gabata.

Mista Wushishi ya bayyana cewa, an dauki matakai daban-daban na duba kura-kuran jarrabawar, inda ya kara da cewa matakan sun fara samun sakamako mai kyau.

Tun da farko ya sanya ido kan yadda 2023 SSCE ke gudana a jihohin Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa da Bauchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: