Bazoum ya bukaci Amurka da daukacin kasashen duniya da su taimaka wajen dawo da tsarin mulkin kasar Nijar

0 288

Hambararren shugaban jamhuriyar Nijar ya bukaci Amurka da daukacin kasashen duniya da su taimaka wajen dawo da tsarin mulkin kasar bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya.

A cikin wani ra’ayi na jaridar Washington Post, Shugaba Mohamed Bazoum ya ce yana yin rubutun ne a matsayin garkuwa.

Ya kuma yi gargadin cewa yankin na iya kara fadawa karkashin ikon Rasha, ta hanyar kungiyar Wagner da ke aiki a kasashe makwabta.

Makwabtan Nijar da ke yammacin Afirka sun yi barazanar shiga tsakani na sojoji.

A jiya ne hafsoshin tsaron yankin suka kammala wani taro na kwanaki uku a Abuja, inda suka ce sun tsara yadda zasuyi amfani da karfin tuwo kwace mulkin.

A jiya ne dai shugaban kasa Bola Tinubu ya rubutawa ‘yan majalisar dokokin kasar takardar neman goyon bayansu kan wannan takunkumi da kuma daukar matakin soji.

Wasikar tasa ta hada da batun gina sojoji da tura jami’ai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: