Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Biliyan 36 wajen biyan tallafin wutar lantarki cikin watanni uku
Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC, ta ce gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 36 wajen tallafin wutar lantarki a rubu’in farko na shekarar 2023.
A cikin rahotonta na kwata-kwata, Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya NERC ta ce kudaden da gwamantin tarayya take kashewa a kowanne wata wajen biyan tallafin kudin wutar lantarki sun kai Naira Biliyan 12.
Awani labarin kuma Kungiyar likitioci masu neman kwarewa ta kasa, sun bayyana fara gudanar da zanga zanga biyo bayan matsalolin da suka ce suna fuskantar ma’aikatun lafiya ta gwamnatin tarayya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya wacce yanzu haka ke gudanar da yajin aikin sai baba ta gani tace zanga zangar zata fara ne ranar laraba 9 ga watan Augustan da muke ciki da karfe goma na safe. Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwar bayan taron zaman majalisar zartarwa ta bidiyon kai tsaye da kungiyar tayi wacce ta shaidawa babban sakataren ma’aikatar lafiya ta tarayya.