Shugaba Bola Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi biyar masu iyaka da Jamhuriyar Nijar

0 340

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi biyar masu iyaka da Jamhuriyar Nijar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Umar Namadi (Jigawa), Dikko Radda (Katsina), Nasir Idris (Kebbi), Ahmed Aliyu (Sokoto), da Mai Mala-Buni (Yobe).

Kawo yanzu dai ba a bayyana batutuwan da suka tattauna a taron ba, amma watakila taron baya rasa nasaba da kokarin da gwamnatin tarayya da kungiyar ECOWAS keyi domin ganin an maido da tsarin demokoradiyya a Jamhuriyar Nijar.

A jiya Lahadi ne dai, wa’adin da kungiyyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin afrika ta ECOWAS wanda ta baiwa gwamnatin mulkin sojan Nijar na sakin hambararren shugaban kasar Mohammed Basoum ya cika.

Idan zamu iya tunawa dai Kungiyar ECOWAS a yayin taronta na musamman wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a ranar Lahadin da ta gabata a Abuja, kungiyyar ta bai wa masu juyin mulkin wa’adin kwanaki bakwai da su saki shugaban Bazoum tare da maido da tsarin mulkin demokiradiyya.. Shugabannin kasashen yammacin Afirkan sun kuma yi barazanar yin amfani da sojoji wajen fatattakar sojojin juyin mulkin idan har suka gaza biyan bukatun ECOWAS a karshen wa’adin.

Leave a Reply