Kananan hukumomi 171 a jihohi 14 na cikin hadarin kamuwa da cutar Mashako a Najeriya

0 238

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa kimanin kananan hukumomi 171 a jihohi 14 na cikin hadarin kamuwa da cutar Mashako.

Ta ce yankunan da abin ya shafa sun hada da: dukkanin kananan hukumomin dake jihohin Kano, Katsina, Babban Birnin Tarayya, Yobe, Kaduna da Bauchi.

Kananan hukumomi guda 20 da ke jihohin (Gombe, Jigawa, Borno, Nasarawa, Plateau da Zamfara da kuma kananan hukumomi bakwai a jihohin Legas da Osun na cikin wadanda zasu fuskanci wannan cutar..

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa, da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya da kuma abokan hadin gwiwa, ke tattara kayan aiki domin tunkarar barkewar cutar a jihohin.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya Olufunsho Adebiyi, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja jiya, ya ce bayanan da suka samu, sun nuna yadda cutar Mashakon ta bulla a kananan hukumomi 25 da ke Bauchi, Katsina, Yobe da kuma Kaduna wanda yanzu suke a mataki na farko. A cewarsa, jihohi 14 na matakin na biyu, wadanda suka hada da: Katsina, Kaduna, Kano, Yobe, FCT, Bauchi, Gombe, Jigawa, Borno, Nasarawa, Plateau, Zamfara, Lagos da Osun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: