Gwamnatin tarayya ta amince da farfado da kasuwar duniya dake jihar Jigawa

0 447

A wani yunkuri na kokarin samar da ayyukan yi da kuma kara kudaden shiga na jihar a duk shekara, gwamnatin tarayya ta amince da farfado da kasuwar duniya dake jihar Jigawa.

Kasuwar duniyar wadda gwamnatin jihar Jigawa ta kafa a shekarun baya an yi watsi da ita ne sakamakon rashin wadatattun ababen more rayuwa da kudaden lasisin aiki na Dala dubu 300 wadda hukumar kula da sarrafa kayayyakin da ake fitarwa ta Najeriya (NEPZA) take bin jihar tun daga shekarar 2017, da kuma rashin isassun kudaden masu zuba jari da dai sauransu.

Domin farfado da kasuwar hukumar NEPZA da gwamnatin jihar sun cimma matsaya wajen tsara hanyoyin biyan kudaden da aka kashe cikin kankanin lokaci.

Manajan Daraktan NEPZA, Farfesa Adesoji Adesugba, da yake tsokaci a lokacin da gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Nnamdi, ya kai masa ziyara a Abuja, ya shaida wa gwamnan cewa hukumar za ta yi duk mai yiwuwa domin farfado da kasuwar a jihar, nan gaba kadan. A nasa jawabin, Nnamadi ya shaidawa shugaban NEPZA cewa ziyarar ta kasance mai matukar muhimmanci ga tawagar jihar domin samun karin ilimi da kuma bayanai daga hukumar kan hanya mafi dacewa ta farfado da kasuwar da nufin samar da karin kudaden shiga ga jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: