Majalisar dattawa ta tantance mutane 45 da za’a nada ministoci

0 267

Majalisar dattawa ta tantance mutane 45 za a nada ministoci daga cikin jerin mutane 48 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike mata.

Tantancewar ta biyo bayan duba na tsanaki da kuma amincewa da majalisar ta yi a zaman ta na jiya.

Wanda aka tantance sun hada sanata Abubakar Kyari daga jihar  Borno, Abubakar Momoh daga jihar Edo, Nyesom Wike na jihar Rivers, da Farfesa Joseph Utsev na Benue state, Sanata John Enoh daga jihar Cross River.

Sauran sun hada da Dakta Olubunmi Tunji-Ojo daga jihar Ondo, Dakta Betta Edu na jihar Cross River, Imaan Sulaiman daga jihar Nasarawa, da kuma  Ahmed Dangiwa na Katsina da Uche  Nnaji daga Enugu.

Ministocin sun hada da Bello Muhammad daga jihar Sokoto, da tsohon gwamnan jihar jigawa Muhammad Badaru Abubakar, da Yusuf Tuggar na jihar Bauchi, da Kuma Uju-Ken Ohaneye daga jihar Anambara, da sauran su.

A jawabin sa, shugaban majalisar Godswill Akpabio, ya godewa yan majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen gudanar da aikin.

Ya kuma ce yanzu haka zauran majalisar ya tantance mutane 45 daga cikin 48 wanda shugaban kasa ya aike musu.

Gidan radio sawaba ya rawaito cewa ba’a tantance tsohon gwamnan jihar Kaduna ba, Malam Nasiru El-Rufai, da Abubakar Danladi daga jihar Taraba da kuma babban daraktan raya bankunan kasuwanci Stella Okotete wanda har yanzu aka jiran jami’an tsaro su wanke su kafin a tantance su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: