Idan matatar Dangote ta fara aiki Nijeriya ba za ta kara bukatar shigo da man fetur ba

0 202

Gwamnatin tarayya na iya rage kusan Naira Trilyan 6.2tn na kudin shigar da man fetur duk shekara idan matatar man Dangote ta fara siyar mai kamar yadda shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote yayi alkawari.

Dangote, a yayin da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na shugabanin Afirka da aka gudanar a Kigali na kasar Rwanda a ranar Juma’a, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, biyo bayan tsare-tsaren da aka tsara na matatar man Dangote, Nijeriya ba za ta kara bukatar shigo da mai daga wata mai zuwa ba.

A cewar Dangote, matatar man da  zata samar da dalar Amurka biliyan 20 za ta iya biyan bukatun man fetur da dizal a yammacin Afirka, da kuma bukatar man jiragen na nahiyar Africa.

Ya kara da cewa Najeriya ba ta da bukatar shigo da wani abu baya ga man fetur, kuma zuwa watan Yuni, bai kamata Najeriya ta shigo da wani abu kamar mai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: