Rundunar sojin  Najeriya ta kubutar da akalla  mutane 386 daga dajin Sambisa

0 191

Rundunar sojin  kasar nan ta ce a jiya Lahadi kubutar da akalla  mutane 386, galibi mata da kananan yara daga hannun mayakan Boko Haram da ke dajin Sambisa a jihar Borno.

Babban hafsan riko na runduna ta 7, Brig. Janar AGL Haruna, ya ce an kubutar da mutanen ne a wani samame na kwanaki 10 da aka yi a Dajin Sambisa.

A cewarsa, wasu daga cikin wadanda aka sace sun kasance a hannun ‘yan ta’adda na tsawon shekaru 10 kafin a ceto su a karshen makon.

Brig. Janar , wanda ya zanta da manema labarai a karamar hukumar Konduga, ya bayyana cewa atisayen da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111” shi ne share dajin Sambisa daga ragowar dukkanin ‘yan ta’adda tare da ba wa wasu daga cikin su damar mika wuya. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: