Adadin wadanda sukayi rajistar katin dan kasa na NIN ya kai 107,338,044

0 188

Ya zuwa yanzu adadin wadanda sukayi rajistar katin dan kasa na NIN ya kai dubu 107,da dari 338,da 044 zuwa ranar Juma’a da tagabata , wanda ya nuna karuwar adadin zuwa miliyan 13.2 daga miliyan 104 da aka samu a watan Disamba 2023.

Darakta Janar ta Hukumar Ba da Shawarwari ta Kasa (NIMC), Abisoye Coker-Odusote, wanda ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, ta kara da cewa shirin hukumar na bullo da katin NIN ya kamata ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan damar.

Coker-Odusote ta shaida wa manema labarai cewa suna aiki ne wajen daidaitawa da hada bayanan dukkan hukumomin gwamnatin tarayya domin gudanar da aiki ba tare da wata matsala ba.

Inda ta kara da cewa hukumar na amfani da NIN wajen daidaita dukkan layukan waya tare da samar da hanyoyin dakile duk wata matsala.

Ta bayyana cewa, a ci gaba da fadada aikin cibiyoyin rajistar, hukumar ta kudiri aniyar hada masu rajista miliyan 200 bayan kammala sabunta tsarinta a hedikwatarta da kuma fadin kananan hukumomi 774 da ake dasu fadin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: