Akalla mutane 200 masu bukata ta musamman ne suka amfana da tallafin N2,000,000 a karamar hukumar Guri

0 262

Akalla mutane 200 masu bukata ta musamman ne suka amfana da tallafin Naira Milyan 2 a karamar hukumar Guri, wanda Sanatan Jigawa ta gabas Ahmed Abdul Hamid ya samar.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Muhd Aliyu ne ya bayyana haka yayinda yake yiwa manema labarai karin bayani dangane da kudin a sakatariyar karamar hukumar ta Guri.

Mataimakin shugaban karamar hukumar wanda ya wakilci shugaban karamar hukumar Shu’aibu Muhammad Guri yace kowanne mai bukata ta musamman zai samu tallafin kudi Naira dubu 10 a matsayin tallafi.

Ya bayyana jin dadin sa dangane da yadda Sanatan masarautar Hadejia ya bada wannan tallafin a kokarin da yake na tallafawa gwamnatin jiha. Ya kuma kara da cewa kudin da aka baiwa mutanen masu bukata ta musamman zai rage musu radadin tsadar rayuwa da aka shiga biyo bayan janye tallafin man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: