Yarjejeniyar iskar gas tsakanin Najeriya da Jamus zata Inganta wutar lantarki nan da shekarar 2024

0 230

Ministan Harkokin cikin gida Ambasada Maitama Tuggar, yace yarjejeniyar iskar gas tsakanin Najeriya da Jamus, zata Inganta wutar lantarki nan da shekarar 2024.

Maitama Tuggar ya fadi haka ta Bidiyo kai tsaye a Birnin Berlin na kasar Jamus a jiya.

A shekarar 2018 Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi alkawarin fadada wutar lantarkin kasar nan zuwa Maigawat dubu 25 nan da shekarar 2025,yayinda ya kulla yarjejeniyar makamashi tsakanin kasar Jamus da fadar shugaban kasar Najeriya, amma daga bisani aikin ya tsaya

Kazalika, Ministan wanda yana cikin tawagar shugaban kasa da suke halartar taron G20 na kasashe masu tattalin arzikin da Afika a kasar Jamus, yace jarjejeniyar yanzu haka ta dawo aiki. Ministan ya kuma kara da cewa aikin samar da wutar lantarki zai taimaka wajen kammala aikin hanyar Ajaokuta zuwa Abuja, Kaduna zuwa Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: