Akalla Mutane 9 Aka Kashe Yayin Zanga-Zanga A Kasar Senagal

0 96

Akalla mutane 9 aka kashe yayin arangama tsakanin ‘yansandan kwantar da tazoma da masu zanga-zanga a kasar Senagal bayan an daure jagoran ‘yan adawa, Ousmane Sonko, a gidan yari na tsawon shekara biyu.

Ministan harkokin cikin gida, Antoine Diome, shine ya sanar da adadin mutanen da suka rasu yayin taron manema labarai da aka gudanar cikin dare, bayan an kwana ana rikicin a fadin kasar.

Antoine Diome yace an toshe kafafen sada zumunta irinsu Facebook da WhatsApp.

Rikici mafi muni ya auku a birnin kudancin kasar na Ziguinchor, inda Ousmane Sonko yake a matsayin magajin garin birnin.

Hukuncin daurin gidan yarin wanda aka yanke masa ba tare da yana nan ba, zai hana jagoran ‘yan adawan damar tsayaw takara a zaben badi. An same shi da laifin dabi’u marasa kyau amma an wanke shi daga zarge-zargen aikin fyade.

Leave a Reply

%d bloggers like this: