Gwamnan Jihar Filato Ya Bukaci A Dauki Mataki Kan Kalubalen Dake Fuskantar Maniyyatan Jihar A Kasar Saudiyya

0 140

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bukaci a dauki matakan domin magance kalubalen dake fuskantar maniyyatan jihar a kasar Saudiyya.

An bayar da labarin cewa an samu fargaba tsakanin mahajjata kasancewar babu wani likita cikin tawagar alhazan kimanin 900 da suka tashi daga Bauchi saboda gwamnatin jihar ta kasa biyan kudin likitocin.

Caleb Mutfwang ya bayyana cewa walwalar da jin dadin ‘yan jihar, musamman maniyyatan dake aikin hajji, na da matukar muhimmanci ga gwamnati.

Daraktan ayyukan na hukumar jin dadin alhazan jihar Filato, Alhaji Isa Hamshimu, wanda ya yiwa gwamnati bayanin halin da ake ciki daga Makkah, Saudiyya, yace an kammala shirye-shiryen tabbatar da kiwon lafiyar mahajjata a lokacin da suke Makkah. Yace duk da rashin likitoci da masu wa’azi cikin tawagar alhazan a Makkah, ‘yan asalin jihar Filato dake rayuwa a birnin mai tsarki, suna kula da halin da ‘yan jiharsu suke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: