Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, Ya Sha Alwashin Samar Da Dukkan Kayan Aiki Ga Hukumomin Tsaro A Jihar

0 128

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sha alwashin samar da dukkan kayan aikin da ake bukata ga hukumomin tsaro domin ba su damar gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata a jihar.

Gwamna, cikin wata sanarwa daga babban sakatarensa na yada labarai, Muhammad Lawal Shehu, ya bayyana damuwa tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali akan tsaro da zaman lafiya, cikin kudirorinta guda 7.

Ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro da su tabbatar sun shirya taro kan tsaro da nufin dabbaka shigar da al’umma tare da wayar da kan jama’a akan tsaro da zaman lafiya. A nasu bangaren, shugabannin hukumomin tsaro sun tabbatarwa da gwamnan jajircewarsu wajen dawo da zaman lafiya a yankunan dake fama da rikici, musamman kananan hukumomi 8 da rikicin yafi kamari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: