Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi Ya Kafa Kwamitin Binciken Asusun Fansho

0 88

Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ya amince da kafa wani kwamiti mai mambobi 28 da zai yi nazari tare da tantance hukumar asusun fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomi.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Hussaini Ali Kila ya sanyawa hannu a jiya.

Sanarwar ta ce tsohon shugaban ma’aikatan, Alhaji Mustapha Aminu ne zai yi aiki a matsayin shugaban kwamitin, yayin da shugaban ma’aikatan gwamnati mai ci Hussaini Ali Kila shi ne mataimakin shugaban kwamitin. Mambobin kwamitin sun hada da, Muhammad Shu’aibu Kiri, tsohon sakataren zartarwa na hukumar asusun fansho, da Hashimu Ahmad Fagam, tsohon sakataren zartarwa na hukumar asusun fansho, da Kamilu Aliyu Musa, sakataren zartarwa na hukumar asusun fansho mai ci, da Muhammad K. Dagaceri, babban sakatare a ofishin sakataren gwamnatin jihar, da Nuhu Haruna, babban sakataren a fishin shugaban ma’aikata, da Abba Mustapha Yola, babban sakatare a ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha ta jiha, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: