Alƙali Ya Tisa Keyar Wani Matashi Gidan Kurkuku bisa Laifin Zamba Cikin Aminci

0 306

Kotun majistire dake zaman shari’arta a Jos ta iza keyyar wani dalibi mai suna John Nanden mai shekaru 22 zuwa gidan kaso, bisa laifin cin amana da kuma cuta.


Alkalin kotun mai shari’a Hannatu Gokwat ta bawa wanda ake tuhumar zabin biyan tarar naira dubu hamsin, tare da biyan diyyar naira dubu 37 ga wanda ya kai shi kara kotun.


Tun da farko dai dan sandan dake gabatar da kara a gaban kotun ne Karim Bashir ya bayyanawa kotun cewa wani mai suna Boniface Nandok ne ya kawo korafi wajen yan sanda a ranar 3 ga watan Mayu.


Bashir yace mutumin ya bashi zinare da kudinsa ya kai naira dubu 37,000 da nufin kulla alaka ta kasuwanci amma daga bisani sai ya tsere.


Kazalika Karim ya fadawa kotun cewa wannan laifi da wanda ake tuhumar ya aikata ya sabawa sashe na 297 da sashe na 309 na kundin laifuka da hukunce hukuncen su na jihar Plateau.

A karshe wanda ake tuhumar ya roki kotun da cewa a yi masa afuwa da yardar Allah ba zai sake aikata makamancin wannan laifi ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: