Al’ummar Najeriya za su fuskanci karin kudin lantarki

0 91

Al’ummar Najeriya za su fuskanci karin kudin lantarki muddin gwamnati ta ci gaba a kan shirinta na janye tallafi da kashi 15 cikin 100.

Yin hakan zai kara jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin yanayi bisa la’akari da hakkin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

A Jiya Talata ne mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya sanar da shirin gwamnatin, yana mai cewa za a yi hakan ne domin a rage kashe kudaden gwamnati.

Idan aka dauki wannan mataki za a rage kashe kudaden gwamnati da kusan dala biliyan biyu da miliyan dari shida.

Ba’a dai  bayyana lokacin da gwamnatin za ta janye tallafin kashi 15 cikin 100n ba. Ko a yanzu ma dai, ba kowa ne yake iya biyan kudin wutar lantarkin ba saboda yadda ta yi tsada duk da cewa farashin ya banbanta daga gari zuwa gari da kuma wasu unguwanni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: