Majalisar wakilai ta yi kira da a kara himma wajen aiwatar da dokar masu bukata ta musamman

0 138

Majalisar wakilai ta yi kira da a kara himma wajen aiwatar da dokar masu bukata ta musamman da gwamnatocin jihohi da hukumomi a fadin kasar nan.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin masu bukata ta musamman, Bashiru Dawodu, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jiya, ya ce hana bukata ta musamman shiga wuraren jama’a ba kawai rashin mutuntawa ba ne, har ma yana kawo cikas ga kokarin da ake yi na aiwatar da dokar masu bukata ta musamman.

Dan majalisar ya yi kakkausar suka ga rahoton nuna wariya ga masu bukata ta musamman a kasa. Ya ce ya zama wajibi kwamitin ya binciki lamarin da sauran abubuwan da ke da alaka da masu bukata ta musamman.

Leave a Reply

%d bloggers like this: