A karon farko cikin makonni da dama, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana wa BBC dalilin rigimar da suka yi tsakaninsa da Gwamnan jiharsa ta Bauchi da kuma mataimakin Gwamnan.
Tun a baya wasu rahotanni sun ce an samu hatsaniya ne tsakanin Ministan da Gwamna Bala Mohammed, Kauran Bauchi inda har mataimakin gwamnan ya yi yunkurin marin Ministan.
Lamarin dai ya faru ne ranar Juma’a 19 ga watan Afirilu, lokacin da Mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima ke wata ziyara a jihar ta Bauchi.
Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, gwamnatin jihar Bauchi ba ta mayar da martani kan iƙirarin ministan ba.
Ministan ya ce ba kamar yadda wasu ke yadawa ba cewa da mataimakin gwamna suka yi hatsaniya, da ainahin shi gwamnan ne abin ya fara, a lokacin da suna tafiya da mataimakin shugaban kasa tare a cikin motar bas lokacin da mataimakin shugaban ya kai ziyara jihar.
Masu lura da al’amura na ganin cewa ministan na harkokin waje zai fafata da takwaransa ministan lafiya Farfesa Ali Pate, wanda ya bayyana cewa a shirye yake ya bauta wa al’ummar jihar, wajen neman tsayawa jam’iyyar APC wannan takara.
Duk wanda ya samu tikitin yi wa jam’iyyar ta APC takarar gwamnan a zaben 2027 zai fafata ne da, wanda Gwamna Mohammed ya mara baya ya gaje shi wajen yi wa PDP takara. Masu lura da siyasar jihar na ganin mataimakin gwamnan ka iya kasancewa wanda zai samu wannan gata daga gwamnan.