Shugaban JAMB ya nemi afuwa kan kurakuran da suka faru a yayin jarrabawar da aka gudanar a bana

0 278

Magatakardar hakumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya nemi afuwa kan kurakuran da suka faru a yayin jarrabawar UTME da aka gudanar a bana. Yace ya ɗauki alhakin dukkan matsalolin da suka shafi jarrabawar da aka kammala kwanan nan, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Bwari jiya.

Farfesa Oloyede ya tabbatar da cewa ɗalibai 379,997 da abin ya shafa za su samu saƙon kar-ta-kwana na SMS kafin yau Alhamis, domin su sake bugo takardun shaidar jarrabawarsu, don sake rubuta jarrabawar a ranar Juma’a da Asabar.

Ya bayyana cewa matsalolin sun samo asali ne daga sabbin na’urorin lissafi da wani kamfanin ba da sabis ya kasa girkawa yadda ya kamata, lamarin da ya janyo rudani da fushi daga wajen ɗalibai da iyayensu. Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.9 da suka zauna jarrabawar, sama da miliyan 1.5 sun kasa samun maki 200. Daga cikin 1,955,069 da aka tantance, ƙalilan 4,756 ne kacal suka samu maki 320 ko sama da haka, yayin da rabin ɗaliban suka samu tsakanin maki 160 zuwa 199.

Leave a Reply